Daga Hamdan Abdullah
Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta dage karar da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC reshen Kano suka shigar a kan tsagin Sanata Ibrahim Shekarau zuwa ranar Juma’a 21 ga watan Janairu domin sauraren karar.
Kadaura24 ta rawaito wannan kara dai na kalubalantar shugabancin jam’iyyar APC a Kano wanda wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta amince da zaben shigabannin jam’iyyar a matakin mazabu da kananan hukumomi da na jiha wanda bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar wanda ya samar da Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaba.
A biyo mu nan gaba domin karanta cikakken labarin