Dandalin sada zumunta na Twitter ya bayyana jin daɗinsa game da matakin gwamnatin Najeriya na dawo da ayyukan shafin a ƙasar bayan wata bakwai.
“Mun ji daɗi ganin cewa mutanen Najeriya na iya amfani da Twitter,” a cewar kamfanin.
“Muna matuƙar son yin aiki a Najeriya, inda ake amfani da Twitter don kasuwanci da sadar da al’adu da kuma tattaunawa,” in ji Twitter cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinnsa na dandalin ranar Alhamis.
A ranar Laraba ne wata sanarwa daga fadar gwamnati ta ce Shugaba Buhari ya amince a cire haramcin amfani da Twitter daga 12:00 na daren Laraba.
Gwamnati ta rufe shafin ne a watan Yunin 2021 bayan ya goge wani saƙo na Buhari kan ‘yan bindigar da ke tayar da hankali a yankin kudu maso gabashin ƙasar, tana mai zargin kamfanin da yaɗa labaran “raba kan ƙasa”.