Da dumi-dumi : Yan adaidaita Sahu sun janye yajin aikin da suka tsunduma

Date:

Daga Aminu Abba

 

Gamayyar ‘yan adaidaita Sahu a jihar kano sun janye yajin aikin da suka tsunduma tun ranar litinin din data gabata sakamakon wani zama da akai da bangarensu da na gwamnati karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano Barr. Mahmoud Gadanya.

 

Kadaura24 ta rawaito Barr. Abba Hikima dai shi ne ya wakilci bangaren yan adaidaita Sahun,yayin da Shugaban hukumar karota Baffa babba Dan agundi ya wakilci gwamnatin jihar kano.

 

Yayin zaman an cimma matsaya kamar haka:

1. Za a rubutawa gwamnatin jihar kano takardar Neman ragin kudin sabunta rigistar na naira dubu 8.

2. Yan adaidaita Sahu za su dawo aiki a gobe alhamis.

3 . za a jira gwamnatin ta tsaida matsaya kafin ranar 18 ga wannna wata da za a sake zama.

4 . Yan adaidaita Sahu za su cigaba da biyan Naira 100 harajin kullum-kullum.

Wadannan dai Su ne abun da aka cimma yayin zaman da aka gudanar a yau a ofishin Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano, kuma yayin zaman kowanne bangare ya aminta da duk abubuwan da aka cimma.

1 COMMENT

  1. Hello there! This is my first comment here so I just wanted to
    give a quick shout out and say I really enjoy reading through your blog posts.
    Can you suggest any other blogs/websites/forums that cover
    the same topics? Thank you!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...