Yajin Aikin Yan Adaidaita: PDP a Kano ta zargi Ganduje da Zagon Kasa ga Tattalin Arziki

Date:

Daga Jamila Abdullah Kachalla

 

Jam’iyyar PDP ta jihar kano ta nuna takaicinta, dangane da abun data kirawo zagon kansa ga tattalin arzikin jihar kano da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yake yi sakamakon kin sasantawa da masu tuka babur din adaidata sahu da suka shiga yajin aiki kwanaki uku da suka gabata.

Jam’iyyar PDP ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar na jihar kano Shehu Wada Sagagi ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24

Sanarwar ta ce Kano ta shahara da harkokin kasuwanci daban-daban, kuma adaidaita sahu shi ne babban ginshiki a harkokin sufuri a kano Wanda ya dauki aƙalla kaso 80 na zirga-zirgar yau da kullun a cikin babban birni.

Sagagi yace yana da kyau a lura cewa gwamnatin Ganduje ta gaza wa ‘yan kano ta kowane fanni, musamman ma, yadda gwamnatin ba ta tabuka komai ba a harkar sufuri tsawon shekaru bakwai da ta yi, sai ma lalata tsarin sufurin dalibai da gwamnati ta bullo da Engr Rabiu Musa Kwankwaso ta bullo shi.

Wada sagagi yayi zargin cewa Gwamnatin Ganduje ta mayar da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA wata babbar hukumar tara kudaden shiga maimakon ta zama hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda aka kafata.

“Dubban matasa ne ke gudanar da wannan sana’a kuma tana samar da ayyukan yi da kuma kudaden shiga a jiha, amma gwamnatin da ba ta da kwakkwarar tsarin tattalin arziki tana yakar matasa da mata da sauran mutane masu son dogaro da kawunansu a daidai lokacin da al’ummar kasar ke fuskantar koma baya ta fuskar tattalin arziki da rashin tsaro da ya jefa ’yan kasa cikin matsanancin talauci”.Inji Sagagi

Shugaban na PDP ya yi fatan Gwamnatin zata gaggauta magance wannan matsala domin barin ta zata iya haifara da wani abu daban.

A cikin kwanaki uku na yajin aikin matuka babura masu uku, Kano ta yi hasarar biliyoyin Naira, kasuwanci ya jigata, kuma ofisoshi da dama ba su yi cikakken aiki ba saboda yajin aikin yayin da gwamnatin jihar ke jan kafa wajen daukar wani kwakkwaran mataki da zai iya magance lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...