Daga Zara Jamil Isa
Kungiyar Inuwar Tagwaye ta kasa reshen jihar Kano (Twins forum)
ta gudanar da zaben shugabaninta karo na farko domin sake fasalin shugabancin kungiyar don inganta harkokin ta.
Shugaban kwamitin gudanar da zaben Hassan Isah Muhd Gwale shi ne ya jagoranci zaɓen har ma ya bayyana cewa Engineer Hássan Ahamad Makari a Matsayin sabon Shugaban Kungiyar, sai Kuma Hassan Auwal Muhd Jack city ya zama mataimakin shugaba, An Zabi Hussaini Kabir minjibir a Matsayin sakataren Kungiyar.
Da yake Ganawa da Wakilin Kadaura24 Hassan Isa Gwale ya bukaci wadanda suka samu nasarar a zaben da su yi aiki tukuru domin ciyar da kungiyar gaba.
Ya kuma bukaci wadanda basu samu Nasara a zaben ba, da su marawa wadanda suka samu nasarar baya domin ciyar da kungiyar gaba.
An dai gudanar da zaben ne a makarantar gidan makama da ke nan jihar Kano, inda tagwaye mata da maza daga ƙananan hukumomi arba’in da hudu suka halarci zaben.
Sabbin Shugabannin dai ana sa ran zasu tafiyar da harkokin Kungiyar dai-dai da yadda kundin tsarin Mulkin Kungiyar ya gindawa ba tare da son rai ba.
A Jawabinsa bayan rantsuwar kama aiki sabon Shugaban Kungiyar Tagwayen Engineer Hassan Ahmad makeri ya Wanda yayi Magana a madadin Sauran Shugabannin ya bada tabbacin zasu yi aiki tukuru tare da bujiro da Sabbin dabarun da zasu ciyar da Kungiyar gaba.