Rashin Bashir Tofa Babban Rashi ne ga Kasa Baki Daya – Alhassan Ado Doguwa

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar wakilai Hon Alhassan Ado Doguwa ya bayyana Rashin tsohon Tantakarar Shugabancin Kasar nan a zaben Shekara ta 1993 a Matsayin Babban rashi ga al’ummar Kasar nan baki daya.
Shugaban Masu Rinjayen Wanda shi ne Sardaunan Rano ya bayyana hakan ne Cikin Wata Sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar wakilai Auwal Ali Sufi ya aikowa Kadaura24.
Yace Sardaunan Rano ya kadu sosai Lokacin da ya Sami labarin Rasuwar Guda Cikin Dattawan Jihar Kano Alhaji Bashi Othman Tofa Wanda ya rasu Jiya litinin.
“Bashir Othman Tofa ya bada Gudunmawa sosai Wajen cigaba damokaradiyya da Ilimi a Jihar Kano da Kasa baki daya, don haka cike gibin da ya bari Zai yi wuya a nan kusa”. Hon Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa Dan Majalisar wakilai da yake wakiltar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada yace a madadin Shi Kansa da iyalansa da al’ummar mazabar sa yana Mika Sakon ta’aziyyar sa ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da iyalan mamacin da al’ummar Jihar Kano baki daya.
Sardaunan Rano ya yi fatan Allah ya gafarta tawa Bashir Othman Tofa ya baiwa iyalansa Hakurin jure Wannan gagarumin Rashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...