Kokarin Sulhu da kwankwaso ba Zai Hana mu Mayar Masa da Martani ba – Ganduje

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
 Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ikirarin da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zaben gwamna a 2019 ba , kakabawa Mutane shi akai.
 Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa, sabanin ikirari da ya yi a wata hira da ya yi da wata jarida, Kwankwaso shi ne ya gudanar da magudin zabe, musamman a kananan hukumomi Cikin Birni, inda ya tanadi Mutane galibin su Matasa Suka rika yin zabe ba tare da katin zabe ba.
 Ya ce a fili yake cewa, sa’o’i kadan da fara kada kuri’a aka ce akasarin akwatunan zabe an cika su, sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba, haka tasa dole INEC ta soke sakamakon zaben wasu cibiyoyi da yawa tare da ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
 Malam Garba ya yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda a matsayinsa na shugaba da ke da ruwa da tsaki harkokin zabe, Amma har Yanzu Kwankwaso yana karyata sakamakon zaben da hukumar zabe ta gudanar wanda kuma kotuna suka tabbatar.
 Kwamishinan ya ce kwanaki kadan da suka gabata, Kwankwaso ya kasance a kafafen yada labarai yana gargadin mabiyansa kan yin kalaman da ba su dace ba, amma sai yanzu shi da Kansa ya rika kalaman da ba su dace ba.
 Ya ce bisa ga dukkan alamu, hirar da Kwankwaso ya yi da yan jaridu yana yunkurin lalata gwamnatin Ganduje, Wanda yin hakan watsi ne da batun zaman lafiya da sulhun da ya yi wa mabiyansa wa’azin su yi yan kwanakin baya.
 Malam Garba ya bayyana cewa kamata ya yi Kwankwaso ya gode wa Ganduje bisa kammala ayyukan da ya yi watsi da su, inda ya ce al’ummar Kano na farin cikin tsarin ci gaba na kammala aiyukan da Gwamnatin Kwankwason ta tafi ta barsu.
 Wadannan ayyuka sun hada da  Aminu  Dantata Flyover, titin Yahaya Gusau da Prince Audu Underpass, titin kilomita biyar a cikin kananan hukumomin Dawakin Tofa, Ungogo, Warawa, Rano da Tofa;  Titin Mahmoud Salga, Titin Jaba-Rimin Kebe, aikin samar da wutar lantarki mai zaman kansa a madatsar ruwa Tiga da Challawa da dai sauransu.
 Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa, duk da yunkurin sulhun da ake yi tsakanin shugabannin jam’iyyar, gwamnatin Ganduje za ta mayar da martani ga duk wani yunkuri na yin watsi da nasarorin da ta samu kuma ba za ta shagaltu da ci gaba da gudanar da ayyukan da aka zabe ta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...