Ku Rika girmama Sojoji dai-dai gwargwado, su Kuma su Rika hakuri da ku – Baffa Babba ya fadawa Yan Karota

Date:

Daga Abdulrashid B Imam


 Rundunar Sojoji a kano sun tabbatarwa da kano da hukumar kula da ababen hawa (KAROTA) cikakken hadin kai a yayin da suke kan aikinsu domin samun kyakykyawan sakamako.


 Kwamandan Barikin Sojoji ta Bukaci dake jihar Kano Birgediya.  Janar.  S. Nicodemus shi ne ya yi wannan alkawarin yayin ziyarar girmamawa da ya kaiwa Manajan Daraktan KAROTA, Hon.  Dr. Baffa Babba Dan’agundi domin Inganta alakar aiki matsayinsa na Sabon kwamandan barikin a Kano.


 Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Karota Nabulisi Abubakar K/Na’isa ya aikowa Kadaura24 yace A cewarsa, Kwamandan mai barin gado ya sanar da shi game da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin su saboda haka, yaga dacewar Kai ziyarar don nemi hadin kai da alakar Mai kyau tsakanin Rundunar su day Hukumar Karota.
 Ya tabbatar wa da KAROTA cewa Rundunar za ta ba ta duk wani goyon baya da ake bukata daga Sojojin yayin da ya yarda cewa an kuma yi masa bayani game da rashin fahimtar da ke faruwa tsakanin sojojin da KAROTA yana mai cewa hakan yanayi ne kuma ya kamata a sanar da shi nan take don daukar matakin da ya dace. 
 Nicodemus ya gode wa MD KAROTA da mutanensa kan kyakkyawar tarbar da suka yi masa da fatan samun kyakkyawar dangantaka yayin da ya kasance a Kano.


 A nasa jawabin, Manajan Daraktan na KAROTA ya bayyana cewa hakika hukumarsa tana da kyakkyawar alakar aiki tare da tsohon Kwamandan wanda aka sake tura shi zuwa wani kwamandan da fatan cewa sabon Kwamandan zai ci gaba da aikin.


 Ya ba da tabbacin cewa hukumarsa za ta yi aiki tare da sabon Kwamandan don cigaban Jiha yayin da ya jaddada cewa akwai alakar aiki Mai kyau tsakanin Shugabanin Sojojin da Kuma Shugabanin Karota, Sai yace yawancin  Rikicin da aka samu a baya tsakanin Sojoji da Yan karota galibinbi ana samun sa be da sojoji da ke kan hanya.


 Baffa Babba ya gargaɗi jami’ansa da su riƙa bai wa kowane soja girma dai-dai gwargwado kuma ya yi haƙuri yayin da yake mu’amala da su yayin da duk wata matsala ta samu to su sanar da hukumomin da suka dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...