Daga Abdulrazak Kaura
Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara ta yi Allawadai da abun da wasu matasa su kai na Kai tarnaki a Babban taron jam’iyyar na Jihar Wanda aka lalata wurin da aka Shirya domin gudanar da taron.
Kadaura24 ta rawaito yayin da yake Ganawa da Manema labarai Sakataren yada labaran Jam’iyyar PDP a Jihar ta Zamfara Abba Bello Oando, ya ce Su na zargin matasan daukar nayinsu akai don su hana gudanar da taron nasu, Inda Kuma yace lamari ya yi sanadiyyar salwantar dukiyoyi na miliyoyin Nairori.
Abba Oando yace Matasa sun kwashe kimanin awanni 3 Su na gudanar da ta’addanci a wajen da aka Shirya domin yin taron jam’iyyar ta PDP a Zamfara, Inda suka kone kujeru da rumfuna, da Kayan kawata taron da aka Shirya, baya ga lalata ababen hawan da suka iske a wurin.
” Babban abun takaicin shi ne yadda Yan daban Su ka ci Karen su babu babbaka a wajen ba tare da Jami’an taro sun Kai dauki wajen ba don hana su, tunda aikin su ne kare rayuwaka da dukiyoyin al’umma.” Inji Abba Bello Oando
Yace ya zama wajibi su tunatar da Jami’an tsaron dake aiki a jihar cewa kundin tsarin Mulkin Kasa ne ya basu damar gudanar da taron Kuma sun nemi izinin yin taron, a don haka ya yi fatan Jami’an tsaron zasu rika aikinsu kamar yadda dokar kasa ta yi tanadi.
Sakataren yada labaran na PDP ya yi tir da aikin rashin da’a da matasan sukai, Wanda yace duk wani mutumin kirki dole ya yi Allawadai da abun da marasa kishin damokaradiyya da Jihar Zamfara Suka yi.
Yace Lokacin da jam’iyyar APC ta gudanar da makamancin wannan taron babu Wanda yayi yunkurin hana su ko tayar musu da tarzoma don hana su yin abun da doka ta basu dama, Amma su gashi an yi musu haka Kuma Suna zargi daukar nauyin Matasan akai don su hana su yin taron.
Abba Bello Oando ya yabawa Kafafen yada labarai da yan social media a jihar Saboda yadda suka yayata labarin ba tare da son rai ba, Amma yace jam’iyyar PDP ta Sha alwashin daukar matakan shari’a Wanda kundin tsarin mulkin Kasa ya tanadi don tabbatar da an biya su kudin Kayan da aka lalata musu.