Yanzu-Yanzu: Kwankwaso ya Taya Ganduje Murnar Cika Shekaru 72 a Duniya

Date:

Daga Zara Jamil Isa
 ….ya bayyana shekaru a matsayin masu albarka
 Kwamishinan Ma’aikatar Karkara da Raya Al’ummar Jihar Kano Dr Musa Iliyasu Kwankwaso Sarkin Yakin karaye a madadin ma’aikatan Ma’aikatar ya taya gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 72 da haihuwa.
 Dokta Musa Iliyasu ya ce shekarun da gwamnan ya yi a rayuwarsa masu albarka ne duba da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen daga darajar jihar ta fuskar ayyukan raya kasa daban-daban da aka gudanar a fadin jihar.
 Ya ce a matsayinsa na Gwarzon gwamna na shekara akwai bukatar Sauran Gwamnonin kasar nan su yi koyi da salon MulkinDr Abdullahi Umar Ganduje na cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
 Jami’in hulda da Jama’a na Ma’aikatar Lawan Hamisu Danhassan yace kwamishinan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da yin gangamin zagayawa gwamnatin gwamnan jihar domin ba shi damar ci gaba da gudanar da gagarumin ci gaba ta hanyar samar da karin ababen more rayuwa a kowane lungu da sako na jihar.
 Daga nan sai Kwankwaso ya sake yabawa tare da taya shi murna tare da yi masa fatan alheri, da samun ingantacciyar lafiya da karin Samun albarka a Shekaru masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Daura ya nuna inda za’a binne shi idan ya rasu.

  Mai Martaba Sarkin Daura dake jihar katsina Alhaji Dr....

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...