Rikicin APC: Buhari ya ce baya goyon bayan Wani bangare a Kano

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa
 Fadar shugaban kasa tayi allawada da Wasu labarai da suke cewa Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya na goyon bayan Wani bangare a Rikicin Jam’iyyar APC dake gudana a Jihar kano.
Kadaura24 ta rawaito Shugaba Buhari yace labarin ba gaskiya bane kuma shi  baya Sanya baki a duk Wani al’amari da yake gaban Kotu.
 Cikin Sanarwar da Babban Mataimakawa Shugaban kasa Kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya Sanyawa hannu yace labarin bashi da tushi ballantana makama,don haka ya bukuci al’umma su yi watsi da shi.
Ina Goyan bayan jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya ta, kuma ina so a sami hadin kai,amma ba na goyon bayan kowane bangare a Rikicin Jam’iyyar APC dake faruwa a Jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...