Da dumi-dumi: Dan Zago ya Bayyana yadda Sukai da Shugaba Buhari

Date:

Shugaban wani bangare na jam’iyyar APC a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Ahmadu Haruna Zago, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren Asabar.

Ahmadu Zago, wanda bangaren tsohon gwamnan jihar Sanata Ibrahim Shekarau ya zaba a matsayin shugaban jam’iyyar, ya gana da shugaban kasar ne a yayin da ake ci gaba da rikici kan shugabancin APC reshen jihar ta Kano tsakaninsa da Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Rikicin ya samo asali ne bayan Sanata Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya sun balle daga bangaren Gwamna Ganduje inda suka zarge shi da rashin iya shugabanci.

Hakan ya sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar ta APC a watan Okotoban da ya gabata.

Rikicin ya kai su gaban kuliya kuma a hukuncin da wata kotun tarayya da ke Abuja babban birnin kasar ta yanke ta ce Ahmadu Zago ne halastaccen shugaban jam’iyyar ta APC.

Daga bisani ma, Alƙalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu, ya buƙaci ɓangaren Gwamna Ganduje da ya shigar da ƙara yana neman a yi watsi da shugabancin ɓangaren Shekarau ya biya tarar miliyan ɗaya.

Sai dai jam’iyar ta APC bangaren gwamnatin jihar Kano ta ce har yanzu ba ta karaya ba kuma za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace wajen ganin ta kwace shugabancin jam’iyyar.

‘Buhari ya taya ni murna’

Sai dai a tattaunawarsa da BBC Hausa bayan ganawa da shugaban kasa, Ahmadu Zago, ya ce Shugaba Buhari ya taya shi murnar yin nasarar samun shugabancin APC a jihar ta Kano.

“Shi [Shugaban kasa] ya tambaye ni ‘me aka samu?’, ni kuma na ce masa ‘an samu shugabancin APC a Kano. Daga nan ne ya taya ni murna'”, a cewar Ahmadu Zago.

Amma ya kara da cewa ba su tattauna kan rikicin da jam’iyyar take fama da shi a jihar Kano ba, yana mai cewa “tun da batun yana kotu ba mu tattauna a kansa ba. Ka san shugaban kasa ba ya shiga lamarin da ke gaban kotu.”

Da muka tambaye shi kan jita-jitar da ke cewa akwai yiwuwar su hade da tsohon gwamnan jihar ta Kano, Rabi’u Kwankwaso, Ahmadu Zago ya ce “babu wannan batu. Sai dai ka san ita siyasa babu masoyi ko makiyi na dindindin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...