Daga Abdulrasheed B Imam
Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya yi Wata ganawar Sirri da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago a fadar Shugaban kasa dake Abuja.
KADAURA24 ta rawaito Shugaban Buhari ya gana da Dan zagonne da misalin karfe 09 na daren jiya Juma’a 24 ga watan Disambar 2021, Inda ake ganin sun gana ne game da Rikicin Jam’iyyar APC dake faruwa a jihar Kano.
A dai Jiya Juma’ar Shugaban Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da misalin karfe 3 na rana.