Daga Zara Jamil Isa
Gwamanan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar Kano zuwa Garin Kwankwaso dake Karamar Hukumar Madobi don yin ta’aziyyar Kanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso Kwamaret Inuwa Musa Kwankwaso.
Kadaura24 ta rawaito Idan ba’a mantaba inuwa Kwankwaso Wanda yake shakikin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya rasu ne a Jiya talata ,Inda akai Masa sutura a jiyan kamar yadda addinin Musulci yayi tanadi.
Yayin ta’aziyyar Gwamna Ganduje ya yiwa mamacin addu’a da fatan samun rahamar Ubangiji tare da Allah zai baiwa iyalai da yan uwan Marigayin Hakurin jure rashin.
Hakimin Madobi Makaman Karewa Alhaji Musa Sale Musa ne ya tarbi tawagar Gwamnan tare da godewa Gwamnan bisa ziyarar ta’aziyyar Dan uwansu da yaje musu.