Daga Abdulrasheed B Imam
Disamba 19, 2021
Shugaban Darikar Kadiriya na yammacin Afrika Sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in Allah ya kawo karshen kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Kadaura24 ta rawaito Sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya yi wannan roko ne a yayin wani taron addu’o’i na kasa da aka gudanar a gidan Kadiriya da ke Kano.
Ya ce kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu da sauran sassan duniya na da matukar tayar da hankali, don haka akwai bukatar mutane su dukufa wajen bautar Allah, da neman gafarar sa, tare da guje wa duk wani abu na fasikanci.
Sheikh Karibullah Nasir kabara ya shawarci al’umma da su rungumi addu’o’i a kullum tare da kulla kyakkyawar alaka tsakanin su da Ubangiji Madaukakin Sarki.
“Ya kamata mu koma mu tantance alakar mu da ke tsakaninmu da mahaliccinmu, mu tuba mu guji duk wani abu na fasikanci, mu taimaki mabukata, mu girmama iyayenmu.” Inji karibullah
Malamin addinin musuluncin ya bukaci al’ummar musulmi a duk fadin kasar nan da ma duniya baki daya da su kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a dukkanin sassan duniya.
Ya kuma kara da cewa addu’o’i na musamman kan bala’o’in da suke samun mutane sun samo asali ne tun daga zamanin Manzon Allah (SAW) inda ya kara da cewa ya zama wajibi a gudanar da addu’o’in a wannan mawuyacin lokaci.
Ya ce an umurci tsofaffi, yara, har ma da mata da su halarci irin wadannan addu’o’i na musamman, inda ya bukaci a yada sakon da aka gabatar a lokacin sallah ga wadanda ba su Sami halartar taron ba.
Ya bukaci a yawaita yin alqunuti a dukkanin masallatai da majalisai da Sauran wuraren haduwar al’umma don Allah ya Magance Matsalolin tsaron da ake bukata.
Shugaban Kadiriyya ya lura cewa “idan muka rungumi wadannan addu’o’in, Allah zai amsa addu’o’inmu.”
Yayin da ake gudanar da addu’o’in kasa, an karanta ayoyin kur’ani mai tsarki, kuma an gudanar da addu’o’i na musamman na neman gafarar Allah.