Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da hukumomin Amurka, don fahimtar juna game da zargin Trump na yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

A baya-bayan nan ne shugaban na Amurka ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, matuƙar ba ta tashi tsaye wajen daƙile abin da ya kira kashe Kiristoci a ƙasar ba.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Muhammad Idris, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Najeriya ba ta son yin cece-kuce da Amurka da ma kowace ƙasa.

InShot 20250309 102512486

”Mu mun sani muna da ƙalubalen tsaro a ƙasarmu, amma gwamnatinmu na yin duk mai yiwa domin magance shi”, in ji shi.

Ministan yaɗa labaran ya kuma ce iƙirarin na Shugaba Trump ya ba su mamaki.

”Waɗannan Kiristoci duka muna zaune da su a matsayin ƴan’uwan juna, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya bai wa kowane ɗan ƙasa ƴancin yin addininsa”, kamar yadda ya bayyana.

Barazanar Amuruka: Tinubu ya bukaci yan Nigeria su kwantar da hankulansu

Ministan ya kuma ce a gwamnatin ƙasar na tattauanawa da Amurka, domin lalubo hanyar magance matsalar.

”A gwamnatance akwai hanyoyi da yawa da ake magana da mutanen nan, kuma ina tabbatar wa al’umma cewa za shawo kan wanna matsalar da yardar Allah”, in ji shi.

Sai dai ministan ya kore batun cewa Trump zai gana da Tinubu kan wannan batu.

”Kawo yanzu dai babu wani abu makamancin haka, ama ida suna son ganawa babu abin da zai hana, tun da su biyun duka shuagabnnin ƙasashe ne, amma a yanzu ba a tsaida rana ko lokacin gudanar da hakan ba”, in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...

Barazanar Amuruka: Tinubu ya bukaci yan Nigeria su kwantar da hankulansu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga...