Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗauke Karantar Sakandare ta Mata ta Mai Kwatashi daga titin France Road, Sabongari zuwa unguwar Kaura Goje a karamar hukumar Nassarawa.
Freedom Radio ta rawaito cewa Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya bada umarnin sakewa makarantar matsuguni biyo bayan koken ƴan unguwar Kaura Goje da kewayenta akan zargin yadda ake wa ɗaliban makarantar kwace da sauran su.
Tuni dai kungiyar cigaban unguwannin Kaura Goje, Gwagwarwa, Gawuna, Riga, da Gamar Fulani ta mika sakon godiya ga Gwamna Yusuf bisa cika alƙawarin sauyawa makarantar.
Mazauna unguwannin sun nuna farin ciki yadda aka kai makarantar kusa da su, musamman ma ganin cewa ta mata ce, inda su ka nuna cewa hakan zai kara habaka ilimin mata a yankin nasu.