Sule Lamido, Ya Yi Barazanar Maka Shugabannin PDP a Kotu

Date:

 

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana aniyarsa ta kai ƙara kotu, bayan ya kasa samun fom ɗin da zai saya domin tsayawa takarar kujerar Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa.

Lamido ya bayyana fushinsa ne a safiyar Litinin, lokacin da ya je hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja domin siyan fom ɗin, amma ya ce an hana shi damar sayan form din .

Da yake zantawa da manema labarai a kofar shiga ofishin jam’iyyar, Lamido ya ce yana da cikakken shiri na shiga takarar shugabancin jam’iyyar a babban taron zaɓen shugabanni da aka shirya gudanarwa a ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, a birnin Ibadan, Jihar Oyo.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook tun da farko, Lamido ya bayyana cewa:

“Da ikon Allah, yau Litinin, 27 ga Oktoba, 2025, da ƙarfe 11 na safe, na isa Wadata Plaza hedikwatar jam’iyyarmu mai girma ta PDP domin siyan fom ɗin takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar.”

Sai dai Daily Trust ta rawaito cewa, a makon da ya gabata gwamnonin jam’iyyar PDP sun amince da tsohon Ministan Harkoki na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin ɗan takarar da za su goyi baya domin shugabantar jam’iyyar.

Kafin wannan amincewa, Lamido, Turaki, da tsoffin gwamnonin Kano da Kaduna — Ibrahim Shekarau da Ahmed Makarfi — duk sun bayyana sha’awarsu ta tsayawa takarar wannan kujera.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sauyawa makarantar mata ta Mai Kwatashi matsugunni

Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗauke Karantar Sakandare...

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...

Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce...