Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Date:

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa wata gidauniya mai suna Pyramid of Heart foundation bisa yadda ta da gudunmawar na’urar da dake taimaka marasa Lafiya wajen yin numfashi wato Oxygen Concentrated Machine ga sashin ba da agajin gaggawa na Asibitin.

Shugaban Asibitin Dr. Hussain Muhammad ne ya yi yabon lokacin da ya karbi na’urar.

Dr . Hussain Wanda shugaban ma’aikatan Asibitin Musa Ado Zango ya wakilta ya ce ya zama wajibi a yabawa gidauniya domin aikin da ta yi zai ceto rayukan mutane da dama a Asibitin .

Ya ce tallafin na’urar zai taimakawa kokarin gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na inganta bangaren Kula da lafiyar al’ummar jihar Kano .

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Dr. Hussaini ya bukaci sauran kungiyoyi da ma daidaikun al’umma da su yi koyi da Wannan abun alkhairin da gidauniyar Pyramid Heart foundation domin taimaka kokarin Gwamnati na inganta bangaren Lafiya.

Da yake nasa jawabin shugaban gidauniyar a jihar Kano Shamsudden Sani Mu’azu ya ce sun baiwa Asibiti gudunmawar na’urar ne a kokarinsu na ba da tallafi ga sha’anin Kula da lafiyar al’umma.

Shamsudden Sani ya ba da taccin za su ci gaba da kai ziyara Asibitin domin ganin Irin halin da Asibitin yake ciki da kuma ba da tasu gudunmawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...

RMK@69: Kwankwaso Jagora Ne Mai Hangen Nesa, Abba Kuma Na Kawo Ci Gaba a Kano – Bakwana

Wani jigo a kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon mai ba...