Tun jiya da daddare da yansanda suna kama Dan Jarida Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano al’umma da kungiyoyi daban daban suka rika Neman Yan sanda su saki Dan Jaridar saboda Kamun da aka yi masa ba a yi shi bisa ka’ida ba.
Daga cikin Kungiyoyin da suka nemi a saki Dan uwa Rano har da Amnesty International , inda ta fitar da sanarwa kamar haka:
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Amnesty International ta bukaci ’yan sanda su gaggauta sakin dan jarida Ibrahim Dan’uwa Rano da ke Kano, wanda aka kama bisa zargin ɓata suna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Amnesty International ta fitar a Lahadin nan.
Kungiyar ta ce, kama dan jaridan ba bisa ka’ida ba ne kuma ya saba wa ’yancin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulki ya tanada.
Sanarwar ta bayyana cewa kama dan jaridan saboda aikin jarida da yake yi yana daga cikin alamu na amfani da jami’an tsaro wajen cusgunawa kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.
Ƙungiyar ta ce zargin da rundunar ’yan sanda ta yi cewa dan jaridan na gudanar da gidan talabijin na intanet ba tare da lasisin Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Ƙasa (NBC) ba, yana nuna yunkurin takura ’yancin kafafen yada labarai, domin wannan ba ya daga hurumin NBC..
Amnesty International ta nemi a saki Ibrahim Dan’uwa Rano ba tare da wani sharadi ba tare da janye duk wani yunkuri na tauye ’yancin aikin jarida a ƙasar.
Yanzu haka dai rahotanni sun tabbatar da cewa yan sandan sun saki Ibrahim Ishaq Dan uwa Rano , bayan Kwashe sa’o’i a hannun yan sandan .
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an saki Dan Jaridar ne da misalin karfe 05:30 na ranar lahadin nan, bayan da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya Sanya baki a Maganar.