Hana barace-barace: Gwamnatin Kano ta Gana da Alarammomi

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin Jihar Kano tana cigaba da ganawa da Masu Ruwa da tsaki, a kokarin ta na ganin ta hana barace-barace a birnin Kano da kewaye.

Kwamitin da Gwamnatin ta kafa domin lalubu hanyoyi ko tsarin da za a yi amfani da shi domin hana barar Wanda ke karkashin Jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Kuma shiga hukumar tsarawa da aiwatar da manufofin Gwamnatin Jihar Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya gana da alarammomi daga Kananan Hukumomi 44 dake fadin jihar nan.

Yayin da yake yi musu Jawabi Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi ya ce an tara alarammomin ne domin a fadakar da su yunkurin Gwamnati na hana barace-barace , Sannan Kuma a karbi shawarwari daga garesu domin a gudanar da tsarin ba tare da an musgunawa wusu ba.

Yace Gwamnati ta bijiro da shirin hana barace-baracen ne, ba don ta takurawa Wani ko Wasu ba ,sai dan ta kawo karshen wulakancin da abokan zamanmu suke yi mana na gorin bara.

ina so ku Sani Gwamnati bata da burin hana Karatun alqur’ani don Haka sai ku kula , Saboda Wasu yan Siyasa Suna so su siyasantar da lamarin shi yasa nake sake fada muku, ba mu da shirin hana Karatun alqur’ani sai dai ma mu kara inganta shi”.Inji Bichi

Rabi’u Sulaiman Bichi ya yi Jawabi mai tsawo kan muhimmancin kyautata makarantun alqur’ani da Kuma alfanun Kar bar chanjin Zamani har ma da Sanar da malaman irin gudunmawar da ake bukatar su bayar don Samun nasarar aikin kwamitin.

Da yake nasa Jawabin Manajan Daraktan Hukumar hana barace-barace a jiha kano Ustaz Muhammad Albukari Mika’il yace ana bukatar tattara shawarwarin masu ruwa da tsaki a sha’anin hana barace-baracen don ganin Gwamnati ta yi abun daya dace akan masu barar.

Mun tattauna da rikunoni da dama, amma ku ne kashin bayan tafiyar don haka muka taraku ku zo gabanmu ku bamu shawarwarin hanyoyin da zamu bi mu magance Matsalolin barace-barace da suka addabi al’ummarmu”. Inji Albukari

Muhammad Albukari ya yi alkawarin yin aiki da shawarwarin da alarammomin suka bayar don al’amarin su ya shafa da su da almajiransu.

Bincike ya nuna mafi yawan mabaratan da suke bara a titunan kano ba almajiran tsangayu bane, ya kuma dora kaso Kusan 70 Cikin 100 na matsalar bara a jihar kano akan Iyayen yara, Musamman Waɗanda ake turo su karatu basu Kai Shekaru bakwai ba”. Inji Albukari

A Jawabansu daban-daban Wasu daga cikin alarammomin da suka halarci taro sun bada shawarwarin tare da baiyanawa Gwamnati Cewa sun yi maraba da tsarin, amma suna fata suma za ta cika musu alkawuran da tayi musu tun abaya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...