Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Date:

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of Kano Indigenes Lawyers) ta sake mika buƙatar ganin kasashen duniya sun shiga cikin batun zargin kisan mutane da ake yiwa Hon alasan ado doguwa Dan majalisar tarayya doguwa da tudun wada a karamar hukumar Tudun Wada yayin zaɓen 2023, domin tabbatar da adalci.

Kungiyar ta mika takardu da hotunan shaida zuwa ofisoshin jakadancin ƙasashen America Ingila, Saudi Arabia, Majalisar Dinkin Duniya, da wasu ƙasashe, ta na neman su taimaka wajen ganin an gudanar da cikakken bincike da kuma daukar matakin na shari’a kan lamarin da ya jawo rasuwar mutane da raunuta wasu .

A wata takardar mai dauke da kwanan watan 10 ga watan Octoba, 2025, takardar ta bukaci ofisoshin da aka Kai korafin da su Sani wanyi watsi da lamarin kisan mutanenne saboda wata bukata ta Siyasa.

Haka zalika, a kwanakin baya kungiyar ta kai irin wannan korafi zuwa ofishin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Majalisar Tarayya, da Majalisar Dattawa ta ƙasa, inda ta bukaci gwamnati da hukumomi su tabbatar da adalci ga kowane ɓangare da abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...

Kananan Hukumomin Tarauni Rogo da Doguwa sun zamo koma baya wajen yin rijistar Masu zabe a Kano

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu kananan hukumomin...

Taron Zuba Jari na Bauchi: Sabuwar Damar Bunƙasar Tattalin Arziki – Daga Lawal Muazu Bauchi

  Ga dukkan alamu, Jihar Bauchi na fitowa a hankali...