Rundunar tsaron farar hula (NSCDC) a jihar Kano ta kama wani matashi da ake zargi da fataucin tabar wiwi, tare da mika shi ga Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a kotu.
Kwamandan hukumar a jihar, Comdt. Bala Bawa Bodinga ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar da ke Kano, a jiya Alhamis.
A cewar Bodinga, jami’an hukumar a karamar hukumar Doguwa, bayan samun sahihin bayanan sirri, su ka cafke wanda ake zargi mai suna Yusuf Alasan, mai shekaru 25, mazaunin Doguwa, tare da wasu mutum biyu, Muktar Musa da Musa Sani — a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025, misalin ƙarfe 2:30 na dare.
Ya ce an kama su ne a Kofar Riruwai, a karamar hukumar Doguwa, yayin da suke dauke da buhu cike da tabar wiwi daga garin Doguwa zuwa Kafau, cikin karamar hukumar Doguwa.
“An kammala binciken farko da hukumar ta gudanar, kuma a cikin tsarin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, yau mun mika wanda ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi tare da abokan harkallarsa, da kuma hujjojin da aka kama, ga hukumar NDLEA ta jihar Kano domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan shari’a,” in ji kwamandan.
Bodinga ya jaddada kudirin hukumar NSCDC na kare muhimman kadarorin gwamnati da kuma ci gaba da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da miyagun ayyuka a cikin jihar Kano.
Ya kuma gode wa manema labarai bisa goyon bayan da suke bai wa hukumar, tare da kiran su da su ci gaba da hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.