Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci dukkan rassanta a fadin kasar da su fara yajin aikin gargadi na makonni biyu daga ranar Litinin mai zuwa.
Daily Trust ta rawaito cewa shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya sanar da hakan a yayin taron manema labarai da ake gudanarwa a cibiyar kungiyar da ke Jami’ar Abuja.
Piwuna ya ce an yanke shawarar fara yajin aikin gargadi ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da abubuwan da kungiyar ke bukata.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito kungiyar ta ASUU ta jima ta yiwa gwamnatin tarayya barazanar tafiya yajin aikin.