Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu kananan hukumomin Rogo, Doguwa da Tarauni ne koma bayan wajen yin rijistar Masu zabe da hukumar zabe ta Kasa INEC ta ke gudanarwa.
Rohoton ya bayyana cewa Jimillar mutane 59,203 ne suka kammala rajista a jihar Kano wanda hakan ya sanya Jihar ta zama ta farko a fadin Najeriya wajen yawan masu rajista domin zabe
Shugaban Karamin Kwamitin Nazarin Bayanai da kididdiga na rijistar a kano, wanda kuma yanzu shi ne kwamishinan Kula da harkokin Kiwo na jihar Kano Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fitar cikin wani rahoto da ya fitar kan cigaban da ake samu game da rijistar Masu zabe a Kano.
A cewar rahoton, karamar hukumar Nassarawa ce ta fi yawan masu rajista da adadin 2,442, sai Kumbotso da 2,333, sannan Bichi da 2,328.
Wannan ya nuna karfin yawan jama’a da kuma saukin samun cibiyoyin rajista a yankunan birane.
Rahoton ya kuma bayyana cewa wasu kananan hukumomi da ke tsakiyar matsayi kamar Dala (1,548), Gaya (1,542), Rimin Gado (1,570), da Ungogo (1,632) sun nuna halin shiga rajista cikin matsakaici amma mai dorewa.
Haka kuma, mafi yawan kananan hukumomi kamar Ajingi, Bunkure, da Minjibir sun samu rajista tsakanin 1,000 zuwa 1,200, wanda ya yi daidai da matsakaicin adadin jihar baki daya.
Sai dai rahoton ya nuna cewa Rogo (147), Doguwa (536), da Tarauni (549) sune komawa baya wajen yawan masu yin rajistar.
Dr. Aliyu ya bayyana cewa wannan sakamakon yana nuna cewa akwai babbar dama a yankunan birane wajen rajistar masu zabe, tare da bukatar kara kokari wajen isar da bayanai da kuma tallafin kayan aiki domin karfafa shiga rajista a yankunan karkara da ke da karancin yawan masu rajista.
Sharhi
Sai dai akwai damuwa sosai yadda karamar hukumar Tarauni ta shiga jeren kananan hukumomin da suke komawa bayan wajen yin rijistar .
Karamar hukumar Tarauni dai tana cikin manyan kananan hukumomin kwaryar Birnin Kano da ya kamata ace tana gaba-gaba wajen samun yawan masu yin rijistar.
Akwai bukatar mahukuntan yankin su Maida hankali wajen ganin sun wayar da Kan al’ummarsu don su fita su yanki katin zabe.