Dole Sai Kun Bamu hadin Kai Zamu Sami Nasarar Ilimantar da ‘Ya’yanku – Wani Malami ya fadawa Iyaye

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Anyi Kira ga iyaye dasu maida hankali wajan kula da ilimin ‘ya’yansu domin samun al’umma ta gari .

Shugaban makaranatar Hidayatul rahaman Islamiyya dake unguwa sani mainagge malam salis Ibrahim kofar Na’isa ne ya bayyana hakan yayin bikin saukar karatun Alƙur’ani Mai girma na dalibai 180 Wanda ya gudana Gwale filin mushe .

Malam salis ibrahim yace samar da ingantaccen ilimi shi ne ginshikin cigaban kowacce al’umma, adon haka suke bukatar goyan bayan iyaye domin cimma burin da suka Sanya a gaba.

Babu shakka Malamai Suna iya bakin kokarin su wajen koyar da yara don Haka suma Iyaye sai sun Kara kaimi wajen baiwa Malaman goyon baya domin Samun Nasarar da ake fata” inji Malamin

Malam Salis baa bayyana godiyarsa ga Dan Darman Kano Alh Bello Ado bayero bisa damar da ya samu na halarta bikin saukar karatun duba da dumbin ayyukan da suke gabansa, haka zalika shugaban ya yabawa shugaban karamar hukumar gwale Khalid Diso bisa Alkawarin kammala Aikin makaranta .

wakilin Kadaura24 ta ya bamu labarin cewa taron ya samu halarta shugabani da sauran al’umma da dama daga Ciki da wajen Kano.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...