Al’ummar garuruwan Tokarawa, Gorubai, Garawa, Yarawa da Dan Tsuku da ke cikin karamar hukumar Nasarawa a Kano sun koka kan matsalar rashin hanya da kuma rashin gada da za ta taimaka musu wajen ketare wani rafin da ya kasance babban kalubale ga rayuwarsu.
Mazauna yankin sun bayyana wa wakilinmu cewa tsawon shekaru suna fama da matsalolin zaizayar ƙasa da kuma rashin wadatattun hanyoyin da za su sauƙaƙa musu rayuwa, musamman a lokacin damina.
Daya daga cikin dattawan yankin, Malam Sani Haruna Baba, ya ce sun shafe shekaru suna fuskantar matsalar rashin gada da za ta haɗa su da sauran unguwanni.
“Unguwanninmu babu hanya, babu asibiti, babu hasken wutar lantarki. Mata masu juna biyu kan rasa rayukansu idan aka daukos su zuwa Asibitin Sir Sunusi ko Murtala. ’Yan siyasa kuma sun manta damu a karamar hukumar Nasarawa,” in ji Malam Baba.
Shi ma wani mazaunin yankin, Malam Muhammadu Lawan Garawa, ya bayyana cewa matsalar rashin gada ta haddasa cikas har a al’amuran aure.
Ya ce:
> “Saboda wannan matsalar, mutane basa son zuwa neman aure a garuruwanmu, ga kuma matsalar rashin makarantun da suka dace.”
Shugaban ƙungiyar cigaban al’ummar yankin (INA MAFITA), Shu’aibu Ibrahim Aramma, ya bukaci gwamnatin Kano ƙarƙashin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, da sauran wakilai a matakin jiha da tarayya da su kawo musu agajin gina gada domin rage musu wahala.
“Mai Girma Gwamna, muna roƙon Allah ka zo ka gani da idonka. Muna cikin ƙunci sosai, har akwatin zabe babu a yankinmu, kamar ba Kano muke ba,” in ji Shu’aibu.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar Nasarawa kan wannan batu, amma ya rawaito cewa shugaban ya bukaci al’ummar yankin su kai korafinsu a rubuce.