Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai da abin da ta kira yaƙin neman zaɓe tun lokaci bai yi ba da wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takara ke gudanarwa a shirye-shiryen zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ya bayyana haka a wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya a Abuja, inda ya ce babban ƙalubale shi ne giɓin da ke akwai a cikin dokar zaɓe.
Ya ce dokar zaɓe ta 2022 ta ce yaƙin neman zaɓe na farawa ne kwanaki 150 kafin zaɓe amma ya ƙara da cewa babu hukuncin da aka tanada ga masu karya wannan doka.
Hasashe 6 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kuma suka tabbata a siyasar Kano
Yakubu ya ce wannan ya sa hukumar ba ta iya sa ido kan kuɗaɗen da ‘yan takara da jam’iyyu ke kashewa cikin wannan lokaci ba.

A nasa jawabin, tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya kira yaƙin neman zaɓe tun lokaci bai yi ba a matsayin barazana ga sahihancin zaɓe, inda ya buƙaci a dinga hukunta jam’iyyu da ‘yan takara da suka saba da hakan, musamman masu riƙe da mukaman gwamnati.