Fadar Mai alfarmar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad abubakar na III ta aiyana ranar Litinin 25 ga watan Agusta ta zama 1 ga watan Rabi’ul Auwal 1447.
Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci a Majalisar Sarkin Musulmin kuma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya fitar da bayanin cewa ba a samu ganin jinjirin watan Safar ba a ranar Asabar a Najeriya.

“Kwamitin Ganin Wata na Ƙasa da na Harkokin Addini a Majalisar Sarkin Musulmi ba su samu bayanin fitar sabon watan Rabi’ul Auwal ba a ranar Asabar 29 ga watan Safar.
“Don haka Lahadi 24 ga watan Agusta za ta zama 30 ga watan Safar 1447,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa Sarkin Musulmi ya aiyana Litinin a matsayin farkon watan Rabi’ul Auwal bayan amincewa da rahoton rashin ganin wata da aka bayar.