Gwamnatin Kano na neman Karin runfunan zabe a jihar

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci a samar da karin rumfuman zabe a mazabun jihar Kano domin rage cunkoson da ake fuskanta a lokacin zabe.

Shugaban kwamitin wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zabe kuma kwamishinan yada labarai Comred Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bukaci hakan lokacin da kwamitin ya ziyarci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Amb. Abdu Zango a ofishinsa.

FB IMG 1753738820016
Talla

Comred Waiya ya ce an samu karin sabbin gundumomi da unguwanni a jihar Kano wadanda su ke bukar a shigar da su cikin jadawalin hukumar, inda ya kuma bukaci a rage alkaluman rumfuman da ake samun cunkoso zuwa sabbin rumfunan zaben da za a kirkira.

Ya shaidawa shugaban hukumar cewa kwamitin zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da jihar Kano ta rike kambunta na jihar da tafi kowace jiha yawan al’umma a kasar nan.

Ya kara da cewa a shirye kwamitin yake ya yi aiki kafada-da-kafada da hukumar domin wayar da kan al’umma tare da taimaka musu ta kowace fuska.

A nasa bangaren shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Amb Abdu Zango ya ce akwai sama da katin zabe 360,000 da har yanzu masu su basu zo sun karba na a jihar Kano.

Don haka ya bukaci kwamitin da ya wayar da kan wadanda suka yi rijista su zo ofishin hukumar domin karbar katinsu.

A yayin ziyarar, shugaban kwamitin na tare da wakilai da sakatarorin kwamitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...