Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa ‘yan bindiga sun kona wata motar fasinja dauke da mutum 42.
Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar ayyukan ‘yan bindiga a inda suke.
Wasu shaidu sun cewa BBC lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.
“Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata,” kamar yadda wadanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.
Tuni dai aka yi jana’ziar mamata in ji shaidu.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴan sandan jihar, amma haƙarsu ba ta ci cimma ruwa ba, ko da suka kira kakakin, wayarsa a kashe take.
Kazalika mun kira kwamishinan tsaro na jihar har sau uku shi ma bai ɗauka ba.
Tuni dai aka yi jana’ziar mamata in ji shaidu.