Hukumar zabe mai zamanta ta Kasa ta bayyana Dan takarar Jam’iyyar NNPP Ali Lawan Alhassan a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na dan majalisar Jiha na kananan hukumomin Bagwai da Shanono da kuri’u 16,198.
yayin da dantakarar APC ya samu kuri’u 5,347.
Baturen zaɓen Farfesa Hassan Adamu Shitu ne ya sanar da sakamakon da misalin ƙarfe 12:36am.

Haka zalika hukumar zaben ta bayyana Dan takarar Jam’iyyar APC Garba Yau Gwarmai a matsayin wanda ya lashe zaben Dan Majalisar jiha mai wakiltar kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa a Majalisar dokokin jihar Kano .
Baturen zaɓen yankin, Farfesa Muhammad Waziri, ne ya sanar da sakamakon zaben da ƙarfe 6:10 na safiyar wannan Lahadi.
Farfesa Waziri ya ce jam’iyyar APC ta samu kuri’u 31,472, yayin da NNPP ta sami kuri’u 27,931.
Adan haka ya ce Garba Ya’u Gwarmai, na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen cike gurbin na mazaɓar Ghari da Tsanyawa a majalisar dokokin jihar Kano, da aka gudanar a jiya Asabar .