Za a ci tarar Naira N100,000 kan duk wanda ya sare bishiya a Abuja

Date:

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta ce daga yanzu duk wanda aka samu da laifin sare bishiya zai biya tarar N100,000.

Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin.

Sanarwar ta ambato Daraktar kula da wuraren shakatawa, Mrs Riskatu Abdulazeez, tana kara da cewa “haramun ne sare bishiyoyin da aka dasa a cikin gidajen jama’a ba tare da neman izinin gwamnati ba.”

A cewarta sare bishiyoyin na ta’azzara matsalolin da ke da dangantaka da sauyin yanayi don haka ba za su bari mazauna birnin su ci gaba da sare bishiyoyi ba tare da la’akari da illar yin hakan ba.

“Duk wanda ya sare bishiya ba bisa ka’ida ba zai biya tarar N100,000 kuma za a tilasta masa dasa sabbin bishiyoyi biyu domin maye gurbin wacce ya sare.” in ji Mrs Riskatu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...