Gina Jami’ar MAAUN Da Farfesa Gwarzo Ya Yi Cigaba ne Ga Al’ummar Kasar nan– Sheikh Nazifi Al-ƙarmawi

Date:

Daga Ali Kakaki
Shehin Malamin addinin Musuluncin nan na garin Kano, Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi ya yaba da kokarin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN) dake garin Kano, inda ya ce tabbas ginin Jami’ar ya ginu, kuma komai ya wadatu, kuma abin a yaba wa Farfesa A.A Gwarzo ne bisa namijin kokarin da ya yi wajen kafa Jami’ar domin amfanar mutanen jihar Kano da Nijeriya da duniya ma baki daya.
Sheikh Abdulwahid Muhammad Nazifi Al-ƙarmawi ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai Jami’ar, inda aka zagaya da shi fannoni da bangare daban-daban a cikin Jami’ar dake Kano.
Sheikh Al-ƙarmawi ya bayyana cewa ya Kai Ziyarar ne; “domin kara karfafar harkar ilimi da kuma farin ciki da samun ci gaba wanda Allah ya bamu a kasarmu. Kuma mu ne masu amfanar abin da kuma yaranmu da sauran ‘yan’uwa”, a cewar sa.
Har wa yau a wani bangare na bayaninsa, Al-ƙarmawi  ya ce; “gaskiya wannan Jami’a, jami’a ce wacce na zagaya na ga iya inda muka iya kewayawa, mu ka ga kowanne irin bangare, Alhamdulillah. Abu ya yi, Gini ya ginu, kuma komai ya yi, mun yi addu’a kuma yadda Allah ya gina mana wannan Jami’a, Ubangiji Allah ya gina mana albarka ya zuba hasken Annabi Muhammadu a ciki.
Na cika da farin ciki, Wannan Jami’ar wadda aka Samar a Nigeria Kuma a garin Kano, ko a wata kasa mu ka je mu ka ganta, za mu ji dadi mu yi farin ciki saboda abu ne na amfanar al’umma, kuma ci gaba ne na bayin Allah”. Inji Al-ƙarmawi
Shehin Malamin ya ci gaba da cewa; “shi Farfesa Gwarzo namu ne, Allah ya saka masa da alheri. Kuma ya kara masa karfin guiwa, kuma ya kara karfafarsa a zahiri da badinin niyyarsa ta alkhairi. Domin wannan babu abin da zai janyo irin wannan aikin sai niyya ta alheri da kyawun zuciya. Muna rokon Allah ya saka masa ya kuma kara karfafarsa. Muna rokon Allah ya kara masa shekaru masu yawa, ya tsufa ya yi shekaru masu yawa yana ci gaba da irin wannan aikin da al’umma za ta amfana. Muna rokon Allah ya wanzar da amfanin irin wadannan ayyuka na shi har ya zuwa ranar alkiyama, al’ummar Annabi (S) su dinga amfana da shi” ya yi addu’a.
Kazalika, Sheikh Abdulwahid Al-ƙarmawi, ya ja hankalin al’umma akan muhimmancin neman ilimi, inda ya ce rayuwa baki dayanta ba ta kyau sai da ilimi, inda ya ce akwai bukatar al’umma ta tsaya ta nemi ilimi domin ci gaba; “duk wani abin da ake gani na ci gaban nan, ko wannan aikin, ilimi ne. Saboda haka ina jan hankalin ‘yan’uwa a tsaya a kan ilimi, kuma a tsaya a taimakawa yara musamman iyaye maza da mata a tsaya a ga yara sun tsayawa ilimi domin amfanin ilimi ta duk inda bawa ya bullo dai rayuwarsa ta na shan bamban da marasa ilimi”, ya jaddada.
Ya karfafi iyayen akan muhimmancin neman ilimi ga ‘ya’yansu da cewa; “mun sani cewa Malamanmu sun tabbatar mana da abin da suka gani kuma da abin da suka samu a nassoshi cewa rayuwar mara ilimi, mutuwa ce. Kuma rayuwar mai ilimi, rayuwa ce, kuma mutuwarsa rayuwa ce. Duk wanda ya zama ya samu ilimi, to yana nan da rai, ba zai mutu ba. Domin ko da an ce ya yi mutuwar da ake yi, to ambatonsa da fadin alheransa ba zai kauce ba matukar rayuwa, idan ko ambaton bawa bai kauce ba, to fa bai mutu ba da ilimi”, ya tabbatar.
A karshe ya yi addu’ar wannan jami’a sabuwa da aka gina a Kano, Allah ya amfanar da mutanen Kano da ita; “Kuma Allah ya amfanar da mutanen Nijeriya duka da ita. Allah ma ya amfanar da dukkanin mutane na duniya da wannan Jami’a ta mu mai albarka. Kuma Allah ya kara taimako. Allah Ubangiji wannan ziyara tamu, Allah ya karba. Allah yasa ta zama sanadi na fatahi don albarkacin Manzon Allah. Farfesa kuma Allah ya saka masa, mataimakansa, tun daga kai kanka kai Kakaki, da duk mataimaka a wannan Harka, inda duk kuke a duniya, Allah ya dafa muku albarkacin Manzon Allah” ya karkare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...