Da dumi-dumi: Sanarwa ta Musamman daga Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai SKY

Date:

 

Shugaban kamfanin SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai ya ce ba zai iya rike mukamin Uban Gammayya kungiyoyin yan kasuwa na jihar Kano ba, wanda kungiyar ta nada shi makon da ya gabata bayan rasuwar Alhaji Aminu Dantata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da SKY ya sanyawa hannu da kansa kuma Mai magana da yawunsa Kamal Yakubu Ali ya aikowa Kadaura24.

Ya ce mukamin da su ka ba shi Babban Mukami ne da ba zai iya dauka ba, don haka ya yanke shawarar sauka daga mukamin kwanaki uku bayan nada shi.

InShot 20250309 102512486
Talla

Yakasai ya ce “Jama’a muna kara godiya da duk ni’imar da Allah ya yi mana da kauna da ake nuna mana dare da rana da girmamawa da ake mana.

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

“Ina bada hakuri da fatan alheri ga gamaryar kungiyoyi yan kasuwar jihar Kano bisa nadi da suka yimun na shugabancinsu a matsayin UBA NA KUNGIYA da su yi hakuri a kan wannan matsayin ya yi min nauyi bazan IYABA. Amma ina tare da su a duk al’amuransu musamman inda ake bukatar gudunmawata.

“Allahumma Salli Ala Sayyidanan Muhammad wa ala alihi” Ni Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ina mika ta aziyyar ga al’ummar Nigeria gaba daya bisa rasuwar babanmu Alhaji Aminu Alhassan Dantata da sauran mutanen da muka rasa baki daya mace da namiji, Allah ya gafartamusu amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...