Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan daidaita farashin man fetur

Date:

Gwamnatin tarayya ta sanya ranar 23 da 24 ga watan Yuli domin gudanar da taron kasa na masu ruwa da tsaki don tattauna batutuwan da suka shafi farashin man fetur da kuma ƙalubalen samar da shi a sashen kasuwancin man fetur, a yayin da ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu ke kara kira ga kafa dokokin daidaita farashi.

Francis Ogaree, Darakta-Janar na fannin Sarrafa Man Fetur, Shigarwa da Hanyoyin Sufuri a Hukumar NMDPRA, ne ya sanar da wannan taro yayin wani zama na musamman a makon makamashi na Najeriya karo na 24 da aka gudanar a Abuja.

InShot 20250309 102512486
Talla

Ya ce NMDPRA za ta shirya wannan taro, wanda zai haɗa ‘yan kasuwa, masu tace mai, masu aiki da masana’antu da jami’an gwamnati don tattauna kan yadda za a kafa tsarin farashi, samar da kayan aiki (feedstock), da hanyoyin da za a daidaita kasuwar man fetur da aka sake warewa daga tallafin gwamnati.

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Ogaree ya bayyana bukatar yin tattaunawa domin karfafa tsarin farashin man fetur a wannan zamani na bayan cire tallafi.

A yayin jawabi a zaman, Ogaree ya ce hukumar tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki “a wajen taronmu, inda muke magance matsaloli da kuma samar da mafita.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...