Daga Khadija Ibrahim
Al’ummar unguwar Tudun wada Bompai dake karamar hukumar Nassarawa, karkashin jagorancin Sarkin Tudun wada Alh Ibrahim Aliyu sun gudanar da wani gangami na babu sani babu sabo, kan yaki da kwacen waya da haura gidajen mutane da shaye-shaye da ake yawan yi a yankin.
An gabatar da gangamin ne da Dattawan mazabar da dagaci da masu unguwanni da kuma shugabancin Tundun wada Foundation Karkashin Comr Ibrahim Abdullahi Usman.
Kazalika an yi gangamin ne tare da matasa da yan sanda da sojoji da DSS da kuma civil Defence da Hisba da kuma sauran Al’ummar yankin.

Yayin gangamin dagacin Tudun wada Alh Ibrahim Aliyu ya ce sun gudanar da taron ne don nuna adawarsu da yadda harkokin tsaro suka tabarbare a unguwar.
” Mun gaji da abubun da suke faruwa a Wannan Unguwa, don haka muka hada kai gaba dayanmun don yakar wadannan munannan da suke faruwa, kuma yin hakan zai taimaka mana mu magance matsalar da ta addabe mu”. Inji shi
Magance sheye-shaye ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Nugeria – Shugabar LESPADA
Shi ma Shugaban Tudun wada Foundation Alh Ibrahim Abdullahi Usman ya ce ba za su yi Kasa a gwiwa ga wajen ga da duk Hadin kan da ake bukatar domin tabbatar da tsaro a yankin .
Shi kuwa limamin Masallacin Juma’a na Tudun wada Sheikh Imam Nura Imam ya ce matsalar tsaro matsala ce da ya kamata kowa ya ba da tasa gudunmawar don ganin an magance ta.
Fadan daba da kwacen waya da shaye-shaye dai ya zama ruwan dare a jihar Kano, wannan tasa Al’ummar mazabar Tudun wada su ka tashi tsaye domin kare yankinsu dama Karamar Hukumar Nassarawa yayi gangamin zagaye lungu da sako domin gargadi ga matasa da iyaye suja kunnen ya’yansu..