Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a cikin masallacin Annabi Sallallahu alaihiwasallam dake Madina yayin jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata.

Tun bayan da gwamnan Kano ya aiyana cire Sarki Aminu a matsayin Sarkin Kano da kuma dawowarsa don cigaba da Sarautar Kano tare da garzayawa kotun don kalubalantar matakin gwamnan kimanin shekara guda da watanni Kenan Amma ba su taba haduwa ba.

InShot 20250309 102512486
Talla

Sai dai dama mutane sun yi hasashen cewa za su iya gamuwa a Madina saboda gwamnan ya je da tawagarsa haka shi ma Sarki Aminu ya je da ta shi tawagar don halartar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata.

A wani fefen bidiyo da Jaridar Kadaura24 ta gani, mun hangi yadda gwamnan Kano da Sarki Aminun suka gaisha a cikin masallacin Ma’aiki (SAW) bayan an kammala Sallar janaza da aka yiwa Dantata, gwamnan sun hadu da Sarkin ne a hanyarsu ta fita daga masallacin zuwa makabartar baqi’ah inda anan ne aka Binne Marigayin .

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Bayan sun hadu sun Gaisa da juna ta hanyar yin musabaha da a tsakaninsu, sai dai bidiyon bai nunu cewa sun yi wata magana ba.

IMG 20250702 WA0000

Amma mutane da dama sun ji Dadin yadda Lamarin ya faru , Amma Babban abun da aka so gani shi ne haduwar Sarkin Kano na 15 da Sarkin Kano na 16 wato Alhaji Aminu Ado Bayero da Malam Muhammadu Sanusi II saboda dukkaninsu sun halarci garin Madina domin shaida jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata.

Amma dai har yanzu Babu wani labari da ake tabbatar da haduwar Sarakunan Kanon guda biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...