Daga Zara Jamil Isa
Gwamnatin jihar Kano ta ce kwamitin kar ta Kwana da ke yaki da Waɗanda basa biyan hakkin Gwamnati game da filayen da suke Amfani da shi ya rufe wani bene mai hawa daya da ke kan titin Murtala Muhammad wanda ke dauke da ofisoshi da dama ciki har da na wani lauya da ya yi nasara a karar da aka shigar ana kalubalentar zabukan Shugabanin Mazabu ba ai hakan da gangan ba.
Sanarwar da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya Sanyawa Hannu Kuma aka aikowa Kadaura24 ta nuna cewa sabanin yadda kafafen yada labarai ke yadawa, musamman a shafukan intanet, babu wata alaka tsakanin rufe ofishin da sakamakon hukuncin da kotun ta yanke.
Ya ce jami’an kwamitin da ke kula da harkokin amfani da filaye na ofishin kula da filaye na jihar da ke aiki tare da hukumar tattara kudaden shiga na jihar (KIRS) suna gudanar da aikinsu na yau da kullum na tabbatar da biyan kudaden amfani da filaye a wani bangare na yunkurin samar da kudaden shiga na jiha.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, kamar yadda aka samu a ofishin, da ke C14/C16 Murtala Muhammad Way na Isyaka Rabi’u & Sons ne ba na lauya Barr Nureini Jimoh ba ne , yace kwamitin ya rufe ofishin ne bayan da ya sanarwar da Masu ginin a ranar 14 ga Satumba 2021, sannan kuma aka basu takardar gargadi bayan sun kasa biyan kudin na tsawon shekaru biyar (2016 – 2021).
Kwamishinan ya kara da cewa a yayin gudanar da aikin kwamitin ya rufe wasu kadarori guda bakwai da suka gaza biyan kudaden su a ranar 1 ga Disamba, 2021 a kan titin Murtala Muhammad da kuma sauran sassan jihar da suka hada da wadanda ke kan titin gidan zoo da titin Zaria da kuma titin Ibrahim Taiwo.
Ya bayyana cewa, dangane da lamarin, kwamitin ko ofishin ne kawai ke hulda da mai gida ba mai haya ba, ya kuma yi watsi da rahoton da kafafen yada labarai ke alakanta shi da ci gaban siyasar jihar.