Daga Usman Hamza Usman
An umarci daukacin limaman Masallatan juma’a a jihar kano da su Shiryya Hudubar gobe juma’a akan Muhimmancin Zaman Lafiya a tsakanin Al’ummah.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Majalisar Limaman Masallatan juma’a na jihar kano Sheikh Muhammad Nasir Adam ne ya bayyana hakan yayin Ganawarsa da manema labarai .
Sheikh Muhammad Nasir yace zaman lafiya shi ne Kashin bayan cigaban kowace Al’ummah, a don Haka ya baiwa Limaman Jihar Kano Umarnin yin huduba akan hakan.
” Addinin Musulci ya baiwa Zaman Lafiya muhimmanci sosai ,shi yasa ake Kiran addinin a Matsayin addinin Zaman Lafiya, don haka muka bada Umarnin ga limamai dau yi Amfani da damar da Allah ya basu Wajen fadakar da al’umma muhimmancin Zaman Lafiya” inji Sheikh Nasir Adam
Sheikh Nasir Adam Wanda shi ne Babban Limamin masallacin Juma’a na Sheikh Ahmadu Tijjani dake Kofar mata kara da cewa suma limaman Masallatan Unguwanni na Khamsussalawatu dake fadin jihar nan Su cigaba da Addu’o’in Samun Zaman lafiya a jihar kano da kasa baki daya.
Shehun Malamin yayi fatan Samun sauki ga sauran jahohi da kasashen da iftila’in rikici ya addabesu.
I was recommended this blog by my cousin. I am not sure whether
this post is written by him as no one else know such detailed about my
problem. You are incredible! Thanks!