Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya mika takardar mallakar fili ga hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a karkasara dake mazabar Darmanawa, domin gina sabon CIVIL DEFENCE a yankin na karkasara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Tarauni Adamu iliyasu Hotoro ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Ya ce shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya mika takardar filin ne a wani taro na musamman da aka shirya a ranar a unguwar ta karkasara inda ya bayyana cewa wannan fili an ware shi ne domin kara karfafa gwiwar hukumomin tsaro a jihar Kano, tare da bunkasa ayyukan kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan karamar hukumar Tarauni.
Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure ya jaddada cewa samar da Wani sabon ofishin na civil defence a yankin na karkasara zai taimaka matuka wajen magance matsalolin tsaro da shaye shaye dakuma kara kusantar da hukumomin tsaro cikin al’umma.
Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade
Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad ya Kara da cewa wannan mataki ya zama dole a duba yadda kalubalen tsaro ke kara karuwa a sassa daban-daban na jiharnan musanman fadan daba sace sace sayar da miyagun kwayoyi dakuma shansu.
Haka Kuma shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure yace an ware wani filin kusa da Wannan filin Wanda nan gaba kadan da zarar yasami sahalewar Gwamnatin jihar Kano a gina ofishin koyar da sana’oi domin amfanin Alummar garin na karkasara dake yankin karamar hukumar Tarauni.

Daganan yayi kira ga Alummar yankin dasu daina afamani da jita jita a duk wani lokaci da Gwamnati ta bijiro da aiyyukan raya kasa a yankunansu inda yace sai Alumma sun bawa Gwamnanti hadin da goyen baya zata Sami damar kawo aiyyukan cigaba a tsakanin Alummar.
Ahmed Ibrahim Muhammad ya godewa Gwamna Alhaji Abba Kabir yusif da kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Alhaji Tajo othman zaura bisa damar da suke basu wajan kawo aiyyukan cigaba a dukkanin mazabu dake karamar hukumar Tarauni.
Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci
A jawabinsa wakilin hukumar NSCDC ACC Ibrahim Ishaq ya godewa Shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure bisa wannan kyautamai muhimmanci daya bawa Hukumar NSCDC domin Kara fadada ofisoshinsu inda yayi alkawarin cewa hukumar za tayi amfani da filin wajan gina sabon ofishin nasu batare da wata matsala ba domin cigaba da kawo tsaro a yankunan karamar hukumar Tarauni
Shugaban tsaro na hukumar civil defence reshen Karamar hukumar Tarauni CSC Aminu Muhammad ya bada tabbacin ci gaba da jajircewa wajen hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin samar da zaman lafiya mai dorewa ga al’ummar yankin karamar hukumar Tarauni.
A jawabansu daban daban shugaban gamaiyyar cigaban Alummar karkasara Aliyu Sambo da dagacin Darmanawa Umar Bello sunyi murna matuka da yadda shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya Samar da wannnan fili ga hukumar civil defence dan Kara inganta harkokin tsaro a yankin na karkasara da kewayenta da Kuma Samar da filin gina cibiyar koyar da sana’oi a yankin domin koyar da matasa sana’oi domin su zamo masu dogaro da kansu
Sun kira ga jama’ar da su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro domin ganin an samu nasarar magance matsalolin tsaro shaye sheye, fadan daba ,sace sace ,dakuma sai da miyagun kwayoyi a yankunan.