Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, a matsayin hutu domin shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447 Hijira.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma taya al’ummar Musulmi murna bisa samun damar ganin sabuwar shekarar, wadda ke farawa da watan Muharram – watan farko a kalandar Musulunci ta hijira.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya aikowa Kadaura24 a yau Laraba.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da kuma Musulmi gaba ɗaya da su yi duba kan ayyukansu na shekarar da ta gabata, tare da amfani da wannan dama domin yin addu’o’i na zaman lafiya, haɗin kai da cigaba a jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.