JOHESU ta Zabi Sabon Shugaba a Kano

Date:

Daga Kabir Muhd Getso

 

Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta kasa Reshen Jihar Kano JOHESU ta zabi Sabon Shugabanta a Kano.

 

Com Ibrahim Muhammad Maikarfi Shi ne ya lashe zaben da aka gudanar jiya a sakatariyar kungiyar dake cikin Birnin Kano.

 

Comrade Makarfi kafin zabarsa shi ne Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da Unguwar zoma na jihar kano Wato Nursing and Midwifery Association Of Nigeria.

 

Da yake Zantawa da wakilin Kadaura24 Maikarfi ya Godewa Allah bisa wannan dama da ‘ya’yan kungiyar suka bashi na jagorantarsu, Sannan ya sha Alwashin cigaba da jajircewa wajen ciyar da kungiyar gaba.

 

Ya Kuma bukaci hadin Kan ‘ya’yan Kungiyar don su bashi hadin Kan da ya kamata domin ciyar da Kungiyar gaba.

 

Kazalika yayi kira da wadanda suka nemi wannan matsayi basu samu ba da su cigaba da bada tasu gudummuwar wajen ciyar da kungiyar gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...