An Bude Sabon Kantin Namadotex a Kasuwar Kantin kwari Dake Kano

Date:

Daga Zakariyya Adam Jigirya

 

Shugaban Kamfanin Namadotex dake Kasuwar Kantin kwari Alhaji Ahmad Nuhu Sani Namado ya ce wajibi ne Yan Kasuwa su rinka tallafawa Matasa da aiyukan yi domin inganta Rayuwar su da Kuma inganta tattalin arzikin Jihar Kano dana Kasa baki daya.

 

Alhaji Ahmad Nuhu Namado ya bayyana hakan ne Lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a wajen bikin bude katafaren kantinsu Mai Suna “Namadotex” dake Kan Titin IBB a Kasuwar Kantin kwari.

 

Shugaban Kamfanin na Namadotex yace wancan Dalili ne yasa ya Suka Bude Kantin Namadotex domin kyautata Rayuwar Matasa da Kuma Samar da Kaya Masu inganci da rahusa.

 

” A sabon Kantin mu na Namadotex mun Kawo Kayan sawa na alfarma Kamar su atamfa, shadda, yadika, mayafai, da duk Wani nau’i na Kayan sawar maza da Mata Yara da manya”. Inji Namado

 

Alhaji Ahmad Nuhu Namado yace sun yi tsarin saukakawa al’umma Saboda Jama’a su Sami damar yin siyaya a Namadotex Cikin nishadi ba tare da Suna sayan Kaya Suna kunchi ba.

 

A Jawabinsa yayin taron bude Sabon katafaren kantin na Namadotex Shugaban hadaddiyar Kungiyar Yan Kasuwa ta Jihar Kano Alhaji Bature Abdulaziz ya yabawa Namadon bisa Samar da Kantin Wanda yace Zai taimaka wajen rage Masu Zaman banza a Kano.

 

Alhaji Bature Abdulaziz ya Kara da Cewa Kantin Namadotex shi ne Kantin da ya fi kowanne kanti saukin Kaya a Kasuwar Kantin kwari.

 

Don haka ya bukaci al’ummar Jihar Kano Nigeria da Africa dasu Ziyarci Kantin domin yin siyayyar Kaya Masu inganci da saukin gaske.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta sake gina Masallacin da aka kona a Gezawa

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna...

Hukumar shari’a ta Kano ta ladaftar da wasu ma’aikatan kotu

Daga Usman Hamza   Hukumar Kula da Harkokin shari'a ta Jihar...

2027: Malam Shekarau ya bayyana matsayar kungiyarsu kan hadakar yan hamayya a Nigeria

Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim...

Da Ɗumi-Ɗumi: Dangote ya sake rage farashin man fetur

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙarin...