Mun Kashe Daliban Jami’ar kudi ta Kaduna Don Nuna Gazawar Gwamnati – ‘Yan Bindiga

Date:

 Daga Halima M Abubakar


 ‘Yan Bindiga wadanda suka sace dalibai 22 daga Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna, sun ce sun kashe biyar daga cikin wadanda ke hannunsu don nuna gazawar gwamnati.


 Wasu mutane dauke da makamai sun mamaye makarantar a ranar 20 ga Afrilu suka sace daliban bayan sun kashe wani mai gadi.


 Sun gabatar da bukatar miliyan N800 amma kwanaki uku bayan ba a biya musu bukatunsu ba, sun kashe dalibai uku da wasu biyu ‘yan kwanaki baya da Suka gabata.


 ‘Yan bindigar sun sha alwashin ci gaba da kashe daliban ba tare da bata lokaci ba cikin kwanaki kadan har sai an biya musu bukatunsu.
 Amma a wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) yayi da wani shugaban kungiyar ‘yan Bindiga wanda ya bayyana kansa da suna Sani Idris Jalingo, ya ce idan Gwamnatin Jihar Kaduna ko dangin wadanda abin ya shafa suka kasa biyan kudin  kudin fansa na Naira miliyan 100 tare da samar musu da babura kirar Honda iri 10 kafin ranar Talata, sauran daliban za a kashe.


 Jalingo, wanda ya ce iyalan daliban tuni sun biya su Naira miliyan 55, ya yi ikirarin cewa sun yi amfani da kudin ne wajen ciyar da daliban.
 “Mun ji kalaman Gwamnan Jihar Kaduna cewa ba zai biya fansar Daliban ba don kada mu kara sayen karin makamai ba.


 “Ya kuma ce ya fada wa danginsa cewa ba zai biya fansa idan aka yi garkuwa da wani daga cikinsu.  Don haka, muna so mu nuna cewa Gwamnatin Najeriya ta gaza shi ya sa muka kashe daliban, ”inji shi.


 Biyu daga cikin daliban da aka sace wadanda suka yi magana yayin hirar sun kuma yi kira ga gwamnati da iyayensu da su dauki barazanar da muhimmanci.


 Daya daga cikin daliban da aka bayyana a matsayin jikan marigayi Sarkin Zazzau na 18, Shehu Idris, ya yi kira ga gwamnati da ta tattauna da masu garkuwar don kubutar dasu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...