Ku Marawa Tinubu baya don ya ciyar da Kasar gaba – Faizu Alfiindiki ga yan Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Faizu Alfindiki ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnatin shugaba Asiwaju Ahmed Bola Tinubu wajen ciyar da kasan nan gaba.

Alfiindiki ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Kano don bayyana ci gaban da aka samu a Nigeria a karkashin tsarin sabunta fata na shugaban kasa Bola Tinubu.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar Bola Tinubu zai kai Nigeria ga tudun mun tsira inda ya ce “tare za mu sami daukaka da samar da ci gaba,bda kwanciyar hankali a Najeriya.”

Faizu alfindiki ya ce, “Shugaba Tunubu ya jajirce wajen tunkarar kalubalen da aka dade ana fama da su, gwamnatinsa ta na kokari wajen inganta tattalin arziki, da inganta tsaro, da zuba jari don Gina rayuwar al’umma.”

Gwamnatin Kano ta fara biyan tsofaffin kansilolin APC hakkokinsu

Ya bayyana cewa, “Duk da kalubalen da ake ci gaba da samu, ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, shaida ce ga yuwuwar jagoranci mai hangen nesa da kokarin hadin kan shugaban kasa, da magoya bayansa.

“Shekaru biyu a gwamnatinsa, ajandar Renewed Hope ta yi tasiri, wajen kawo gagarumin ci gaba ta fuskar gyare-gyaren tattalin arziki, Samar da ababen more rayuwa, da kuma ayyukan jin dadin al’ummar Nigeria .” Inji Alfindiki

InShot 20250309 102403344

“Ina yaba wa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen fito da tsare-tsaren da da suke kawo cigaba a Nigeria karkashin ajandar sabunta fata da Shugaban ya fito da ita.”

Tsohon shugaban karamar hukumar birni a Kano ya ce “A yayin da muke murnar wannan gagarumin buki, ina kira ga ‘yan Najeriya da su jajirce wajen goyon bayan gwamnatin shugaba Tinubu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...