Tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki ƴan siyasar da ke sauya sheƙa bayan sun gama cin moriyar jam’iyyar, abin da ya bayyana da babban kuskure a siyasance.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a kwanakin baya ne dai wasu daga cikin yan majalisar wakilai da sanatan kano ta kudu suka fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.

Sanata Kwankwaso wanda ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake karɓar wasu ƴan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga ƙaramar hukumar Takai, a gidansa da ke Miller road a birnin Kano.
Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki
A baya-bayan nan ne dai raɗe-raɗi suka yi ta yawo cewa Kwankwason zai koma jam’iyya mai mulki ta APC.
Rabi’u Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya.
Ya ce dama kowanne zabe idan ya zo yana zuwa ne da darussan masu tarin yawa don haka ya ce Kwankwasiyya wani tsari ne da wani bai Isa ya wargaza shi ba, saboda tafiya ce ta akida ba ta kudi ba.