Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi kan al’amuran Siyasa Bashir Hayatu Gentile ya yi suka mai kaushi game da kalaman da tsohon shugaban karamar hukumar birnin Kano Faizu alfindiki ya yi akan gwamnatin Kano.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito faizu alfindiki na fadin cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta cancanci al’umma su sake zabarta a karo na biyu saboda yadda ta ke korar ma’aikata, inda ya ba da misali da ma’aikatan wucin gadi da aka kora a hukumar haraji ta jihar.

A zantawarsa da Jaridar Kadaura24 Bashir Gentile ya ce barnar da Ganduje ya yiwa ma’aikata ko kadan Abba ba zai taba iya yin rabinta ba.
“Manyan sakatarori guda biyar Ganduje ya mayar da su matsayin daraktoci sannan ya zo ya yi musu ritayar dole, hakan ta sa suka tafi kotu kuma kotu ta ba da umarnin a mayar da su, amma Ganduje yaki mutunta umarnin Kotu, sai Abba ne ya mayar da su”. Inji Gentile.
Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki
Ya ce Manyan sakatarori biyar din da Ganduje ya mayar da su baya kuma ya yi musu ritayar dole duk da suna da ragowar akalla shekaru biyar su ne kamar haka:
1. Adau Lawan
2. Aminu Shuaibo Rabo
3. Abdullahi Musa.
4. Muhammadu Danduwa.
5. Umar jalo.
Gentile ya ce Ganduje ya yiwa aikin gwamnati da ma’aikata mummunan illar da bai kamata wani mai goyon bayansa ya fito ya yi magana akan sabgar ba.