Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dr Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba.

A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a jihar Osun da ke kudancin Najeriya.
Hajjin bana: Ya kamata gwamnatin tarayya ta dawo da nada Amirul Hajji na kasa – Sarki Sanusi II
“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.
Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke jihar Kano.