Gwamnatin jihar Kano ta bukaci limaman masallatan juma’a na jihar da su mai da hankali wajen cusawa mutane kishin jihar Kano domin samar da cigaba mai dorewa a jihar.
Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi lokacin rufe taron bitar yini 2 da aka shiryawa limaman masallatan juma’a a jihar.

Ya ce Idan aka cusawa mutane kishin jihar za su rika yin duk wani abu da zai kare kimar jihar, sannan su daina yin abun da zai zubar da darajar jihar a idanun duniya.
Kwamishinan ya yi jawabi mai tsahon dangane da salon yadda gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ke gudanar da aikinsu don inganta rayuwar al’umma.
Gwamnatin tarayya ta aiyana ranar hutun ma’aikata
Ya kuma hori limaman da su daina yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu da ta jihar Kano, inda ya ce gwamnati tana damuwa sosai idan ta ga malamai suna fadin wasu abubuwa da ba su dace ba.
“Bangaren malamai ne kadai ya rage ake gani da kima a kasar Nan, don haka nake fatan za ku kare wannan darajar ta ku, ta hanyar daina furta Kalaman da ba su dace ba”. Inji Waiya
Waiya ya kara da cewa ba a shiryawa malaman bita ba ne don gwamnati ta mallakesu, sai don su San halin da gwamnati ta ke cikin da kuma koyawa musu da barun aikewa da sako kasancewarsu wadanda suke damar fada a ji a cikin al’umma.
” Ba mu ce sai kowa ya zama dan jam’iyyar NNPP ba, mun sani kowa yana da ra’ayinsa kuma ba ce ka chanza ba, kawai abun da muke bukata a ajinku shi ne a rika fadakar da al’umma abun da ya dace”.
Kwamishina Waiya ya kuma yi alkawarin gwamnatin jihar Kano za ta cigaban da fito da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar malaman jihar Kano, sannan ya yi isar da duk sakonninsu ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf domin daukar matakin da ya dace.
Da yake nasa jawabin tun da fari shugaban majalisar limaman masallatan juma’a ta jihar Kano Sheikh Muhammad Nasir Adam ya yabawa gwamnatin Kano bisa shirya musu bitar, sannan yayi fatan gwamnatin za ta yi duba na tsanaki akan duk matsalolin da Limamai ke fuskanta.
Ya kuma bukaci limaman da su yi aiki da abubuwan da suka koya yayin bitar, sannan ya ba da tabbacin nan gaba gwamnatin za ta sake shirya wata bitar ga wasu rukunonin limaman masallatan juma’a na jihar Kano.